Dangote ya bayar da gudunmawar dalat Amurka miliyan $20 ga cibiyar Afrika a Amurka

Dangote ya bayar da gudunmawar dalat Amurka miliyan $20 ga cibiyar Afrika a Amurka

Shugaban gidauniyar Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayar da gudunmawar dalar Amurka miliyan $20 ga wata cibiyar Afrika da ke kasar Amurka.

Daily Nigerian ta rawaito cewar cibiyar ita ce a kan gaba wajen mayar da hankali a kan jibintar al'amuran da suka shafi Afrika da gyara suna da tarihin nahiyar a idon duniya.

Cibiyar wata kafa ce ta kirkira tare da daukaka al'adu da kasuwancin nahiyar Afrika da kuma fito da rawar da Afrika ke taka wa a bangaren raya tattalin arzikin duniya a yanzu da kuma nan gaba.

Bayan amincewa da manufar cibiyar, gidauniyar Bill & Melinda ta yi koyi da Dangote tare da sanar da bayar da gudunmawar dala miliyan $5 ga gidauniyar.

DUBA WANNAN: Masu yi don Allah: Wani mutum ya bayar da gudunmawar $1m ga cibiyar Sheikh Ibrahim Saleh, ya nemi a boye sunansa

Ragowar gidauniya, kungiyoyi da jama'ar da suka bayar da gudunmawa tare da nuna goyon bayan cibiyar sun hada da iyalin Mo Ibrahim, sashen kula da al'adu na birnin New York da sauransu, kuma duk sun hallara a wurin taron kungiyar da aka yi ranar Talata.

Dangote ya bawa gidauniyar gudunmawa ne saboda kaunar da yake yi wa nahiyar Afrika da kuma karrama shi da aka yi ta hanyar saka wa cibiyar sunansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel