Rundunar sojin ruwa tara diban sabbin ma’aikata masu digiri da HND

Rundunar sojin ruwa tara diban sabbin ma’aikata masu digiri da HND

Rundunar sojin ruwa a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba, tace ta fara kwasan sunayen wadanda za su dauka aiki masu rike da matakin karatu na digiri da HND.

A cewar wani jawabi dauke da sa hannun daraktan bayanai na rundunar sojin ruwa, Commodore Suleiman Dahun, ya zama dole duk wadanda ke da ra’ayin aikin ya kasance haifaffen dan Najeriya, sannan su kasance da akalla matsayin digiri na “Second Class Upper da kuka “Upper Credit” a HND.

Tsawon maza kada yayi kasa da mita 1.68, yayinda mata kuma kada su kasance kasa da mita 1.65.

Ya zama dole masu neman aikin su kasance da satifiket din NYSC ko na sallama daga NYSC sannan su kasance tsakanin shekara 22 da 28 a ranar 20 ga watan Fabrairu 2020, sai dai ga mai neman mukamin limami da likitoci wadanda kada su zarce shekara 30 da 40 a ranar 20 ga watan Fabrairu 2020.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Dan Maina ya fito da bindiga domin hana a kama mahaifinsa - DSS

Cikakken bayanin yadda za a shiga tsarin na a shafinsu na wanda aka bude a yanzu har zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba 2019 ga duk wanda ke son neman aikin a yanar gizo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel