'Yan sanda sun kama makasa masu amfani da kayan sojoji

'Yan sanda sun kama makasa masu amfani da kayan sojoji

- Jami'an rundunar 'yan sanda ta musamman mai yaki da fashi da makami ta cafke wasu yan fashin da suka suka addabi jihar Imo

- Kwamishinan 'yan sandan jihar, Rabiu Ladodo, ya jinjinawa shugaban hukumar tare da alfahari da rundunar baki daya

- Daya daga cikin 'yan fashin mai shekaru 22 a duniya wanda aka fi sani da Kaka ya bukaci alfarmar gani mahaifiyarsa

A yayin kama wadanda ake zargin, Kachi Nwalolo mai shekaru 21 da Chukwuebuka Esoga wand aka fi sani da Kaka mai shekaru 21, kwamishinan yan sandan jihar, Rabiu Ladodo ya ce, "Ina farinciki tare da alfahari a halin yanzu da nake yanzu."

Kwamishinan 'yan sandan ya ce, baya da fashi da makami, an san wadanda ake zargin da garkuwa da mutane tare da kashesu.

Ladodo ya ce, baya da neman da 'yan sandan ke ma wadanda ake zargin, har gwamnatin jiha na nemansu.

KU KARANTA: Jarumin maza: Ya bige masu garkuwa da mutane tare da sakin mutane da suka kama

Kamar yadda ya fada, kama manyan masu garkuwa da mutane babbar nasara ce ga hukumar 'yan sandan. Ya jinjinawa shugaban SARS din da cewa rundunar akan aikin kwazon da suka gwada.

Kwamishina 'yan sandan ya ce, "Ina gabatar muku da tsagerun 'yan fashin nan kuma masu kashe mutane a kwankin nan. Ina farinciki tare da alfaharin wannan nasarar. Ina jijina ga shugaban rundunar 'yan sanadan ta musamman masu yaki da fashi da makami na jihar nan, Victor Godfrey, da rundunarsa akan aikin nan da suka aiwatar."

"Sun bayyana cewa da sa hannunsu a fashi da makami da kashe-kashen da ke faruwa. Muna bukatar hadin kai daga jama'a don ganin mun kawo karshen tsageru da 'yan ta'adda a jihar nan." in ji shi.

Daya daga cikin wadanda ake zargin, Kaka, ya ce yana son ganin mahaifiyarsa don neman gafararta akan rashin biyayyarsa.

Kaka ya ce, "Ku taimaka ku kira min mahaifiyata. Inason neman gafararta akan rashin zana da na gari da nayi. Yanayin halayyar mutanen Owerri ce ta saka ni komawa hakan. Ku taimakeni ku kira min mahaifiyata in roketa gafara."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel