Yanzu-yanzu: Gwamna Aminu Waziri ya samu nasara a kotu

Yanzu-yanzu: Gwamna Aminu Waziri ya samu nasara a kotu

A ranar Laraba, kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Sokoto ta tabbatar da gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal. a matsayin zababben gwamnan jihar.

Kwamitin Alkalan uku sun yi fatali da karar jam'iyyar APC da dan takararta, Ahmed Aliu Sokoto.

Yayin yanke hukuncin, shugaban Alkalan, Abbas Bawale, ya ce Ahmed Aliyu da APC sun gaza gabatar da hujjojin nuna cewa an sabawa dokar zabe lokacin zaben da kuma tafka magudi.

Alkali Abbas Bawale ya ce shaidun da APC suka gabatar musamman shaida na goma ance kace ne kawai ba wasu hujjoji masu karfi ba.

Aliyu ya kai karan Tambuwal da PDP kotun zabe domin nuna rashin amincewarsa da sakamakon zaben 2019.

KU KARANTA: Gaskiya ta bayyana yanzu - Ganduje ya yi tsokaci kan nasarar da ya samu a kotu

An gudanar da zaben a ranar 9 ga Maris amma aga gaza kammalawa saboda an yi watsi da kuri'u 75,403 yayinda banbancin kuri'un da ke tsakanin abokan hamayyan biyu 3,413 ne.

Yayinda aka gudanar da zagaye na biyu a ranar 23 ga Maris, gwamna Aminu Tambuwal ya lashe zaben da tazarar kuri'u 342.

A wani labarin mai kama da haka, kotun zaben jihar Kano ta tabbatar da gwamna Abdullahi Ganduje matsayin wanda ya lashe zaben.

Yayinda za'a raba gardama tsakanin Abba da Ganduje a jihar Kano, an mayar da Tambuwal da Aliyu birnin tarayya Abuja saboda tsoron tashin hankalin da ka iya faruwa bayan sanar da sakamakon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel