Badakalar N2bn: DSS ta mika Maina zuwa ga hukumar EFCC

Badakalar N2bn: DSS ta mika Maina zuwa ga hukumar EFCC

Kasa da kwanaki uku bayan kamunsa, hukumar tsaro na sirri (DSS) ta mika tsohon shugaban hukumar fansho na kasar, Mista Abdulrasheed Maina ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC).

An mika Maina ga hukumar yaki da rashawar da misalin karfe 5:30 na yamma.

An tattaro cewa ana gasa wanda ake zargin akan zargin hamdame naira biliyan biyu.

An kuma tattaro cewa ana tambayar Maina akan zabin kadarori a Kado Estate da ke Abuja, wasu kadarori a Kaduna da kuma babban gona a Keffi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamna Yahaya ya zabi ‘yar Goje da wasu 17 a matsayin kwamishinoni

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar tsaro na sirri ta tabbatar da kamun Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar fansho.

Peter Afunanya, kakakin rundunar ya tabbatar da kamun a wani jawabi da ya saki a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba.

Yace an kama Maina ne a wani otel a Abuja a ranar 30 ga watan Satumba, 2019, cewa dansa yayi kokarin bude wuta akan jami’an DSS da suka aiwatar da aikin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel