Hukumar EFCC ta kama jami'an INEC 4 da laifin satar N84.7m a Zamfara

Hukumar EFCC ta kama jami'an INEC 4 da laifin satar N84.7m a Zamfara

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC reshen jihar Sakkwato, ta samu nasarar cafke wasu ma'aikata 4 na hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC a jihar Zamfara, bisa zarginsu da almundahana.

EFCC ta ce ta cafke jami'an hudu da laifin yin sama da fadi da kudin biyan gumin ma'aikatan zabe na wucin gadi wanda jimillarsu ta kai kimanin naira miliyan 84.6.

Hussain Ja'afar da Abdulmumin Usman
Hussain Ja'afar da Abdulmumin Usman
Asali: UGC

Hassan Sidi Aliyu da Abdullahi Yusuf
Hassan Sidi Aliyu da Abdullahi Yusuf
Asali: UGC

Wannan rahoto na kunshe cikin wata sanarwa da kakakin EFCC Mista Wilson Uwujaren, ya gabatar yayin ganawa da manema labarai a ranar Laraba cikin ofishin hukumar dake birnin Shehu.

Abdullahi Nasiru, mutumin da ya shigar da korafin jami'an a ofishin EFCC a madadin sauran ma'aikatan zaben jihar Zamfara na wucin gadi, ya ce an hana su N6,000 kudin alawus din abun hawa a babban zaben kasa kashi biyu da aka gudanar a bana.

Kazalika Malam Nasiru ya yi zargin cewa an samu banbanci adadin kudin aikin zabe da aka biya su a jihar Zamfara idan aka kwatanta da sauran jihohi.

KARANTA KUMA: An yi tiyatar dashen koda 60 a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wani bincike ya nuna cewa an biya ma'aikatan INEC wucin gadi a Zamfara N9,000 yayin da a sauran jihohi irinsu Sokoto, aka biya su N12,000.

Uwujaren bayan gabatar da sunayen jami'an na INEC da suka shiga hannu; Hussain Ja'afar, Hassan Sidi Aliyu, Abdullahi Yusuf Abubakar da kuma Abdulmumin Usman, ya ce za a gurfanar da su gaban kuliya da zarar bincike ya kammala.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel