Akwai hukuncin da har yanzu kotu ba ta tabo ba kan laifukan da ake tuhumar Sowore, Dasuki da El-Zakzaky

Akwai hukuncin da har yanzu kotu ba ta tabo ba kan laifukan da ake tuhumar Sowore, Dasuki da El-Zakzaky

- Fadar shugaban kasa ta ce, Sambo Dasuki, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da Omoyele Sowore na ci gaba da shan dauri a saboda kotu ba tabo wasu hukunce-hukunce na laifukan da ake tuhumar su ba

- Hadimi na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan harkokin da suka shafi al'umma, Ajuri Ngelale, shi ne ya bayyana hakan

- Ngelale ya ce kotu ta bayar da beli a kan wasu tuhumce-tuhumce da ke kan ababen zargin a yayin da ba tabo wasunsu ba

- Hadimin shugaban kasar ya yi Allah wadai da zanga-zangar juyin juya hali wadda Sowore ya shirya

Fadar shugaban kasa ta fidda bayani dangane da dalilai da suka sanya ya zuwa yanzu duk da umarnin kotu, ba ta saki tsohon mai ba da shawara kan harkokin tsaron kasa ba, Sambo Dasuki, shugaban mabiya akidar shi'a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore.

Sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar ta bakin hadimi na musamman ga shugaban kasa a kan harkokin da suka shafi al'umma, Ajuri Ngelale, ya ce ana ci gaba da tsare ababen zargin uku saboda kotu ba ta tabo wasu hukunce-hukunce na laifukan da ake tuhumar su ba.

Furucin Ngelale na zuwa ne yayin wata hira da manema labarai na jaridar Legit.ng da ta gudana a ranar Alhamis, 3 ga watan Oktoba.

KARANTA KUMA: Tazarcen Buhari a 2023: Buhari zai yi amai ya lashe kayansa - Buba Galadima

Hadimin shugaban kasar ya ce a yayin da kotu ta bayar da beli a kan wasu tuhumce-tuhumce da ke kan ababen zargin, ya zuwa yanzu ba tabo wasunsu ba, lamarin da ya sanya ba za'a kwance sarkar da aka daure masu laifin uku ba.

Ngelale ya kuma yi Allah wadai da tsohon dan takarar shugabancin kasa na zaben 2019 a jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, jagoran wadanda suka assasa maudu'in aiwatar da zangar-zangar juyin juya hali, lamarin da ya ce 'yancin bayyana ra'ayi yana da iyaka.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel