Shugaba Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa ga al'ummar Musulman Yarbawan Najeriya kan rasuwar shugabansu

Shugaba Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa ga al'ummar Musulman Yarbawan Najeriya kan rasuwar shugabansu

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa ga majalisar kolin shari'ar Musuluncin Najeriya kan rasuwar mataimakin shugaban majalisar, Alhaji Sakariyahu Babalola.

Buhari ya aika wannan sakon ne ta mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, a ranar Laraba a birnin tarayya Abuja.

Hakazalika Buhari ya mika sakon makoki kan iyalai, abokai da al'ummar kasar Yarbawa kan rashin babban dan kasuwa kuma wanda ya bautawa jama'arsa.

Buhari ya bayyana irin gudunmuwar da Alhaji Babalola ya baiwa addinin Musulunci musamman a matsayinsa na shugaban al'ummar Musulman Yarabawan Najeriya.

Kana, shugaban kasan ya ce al'umma za ta tuna Alhaji Babalola matsayin mutum mai son zaman lafiya, mai mutunci da yawan kyauta.

A karshe, Buhari ya yi addu'a Allah ya jikansa da rahma.

KU KARANTA: Gaskiya ta bayyana yanzu - Ganduje ya yi tsokaci kan nasarar da ya samu a kotu

Allah ya yiwa mataimakin shugaban majalisar koli ta shari'ar Musulunci a Najeriya kuma shugaban al'ummar Musulman Yarbawan Najeriya, Zakariyyau Babalola, rasuwa.

Imam Babalola ya kasance ajjajirin mai kudi kuma mai kyautatawa jama'a da dukiyarsa. Shine shugaban kamfanin Telemobile Nigeria Limited.

Shugaban, wanda ya kasance mataimakin sarkin Musulmin a NSCIA, ya mutu a jihar Legas yana mai shekaru 85.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel