Kotu ta sanya ranar yanke hukuncin zaben gwamnan Bauchi

Kotu ta sanya ranar yanke hukuncin zaben gwamnan Bauchi

Kotun zaben gwamnan jihar Bauchi ta sanya ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba a matsayin anar yanke hukunci a karar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takararta na gwamna, Muhammed Abdullahi Abubakar suka shigar.

Jam’iyyar ta APC da dan takararta na gwamna na neman kotun ta kaddamar dashi a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 9 ga watan Maris, 2019 wanda aka kammala a ranar 23 ga watan Maris, 2019.

Mai kara ya kuma roki kotu, da ta soke zabe a rumfunar zabe 336 a kananan hukumomi uku na Bauchi, Tafawa Balewa da kuma Bogoro.

Alkalin da ke jagorantar kwamitin kotun mai mutum uku, Justis Salihu Shuaibu, ya sanar da ranar yanke hukuncin jim kadan bayan ya saurari bangarorin biyu da korafe-korafensu. Daga bisani sai ya dage zaman.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Dan Maina ya fito da bindiga domin hana a kama mahaifinsa - DSS

A gefe guda, mun ji cewa Shari’ar da ake yi tsakanin jam’iyyar APC mai mulki da kuma PDP mai adawa ta zo karshe a kotun farko da ke sauraron korafin zaben bayan da Alkali ta yi watsi da karar da PDP ta shigar. Kotu ta tabbatar da nasarar da Abdullahi Ganduje a zaben gwamnan jihar Kano da aka yi a watan Maris.

Hakan na zuwa ne bayan ‘dan takarar PDP, Abba Kabir Yusuf ya kalubalanci nasarar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel