Gaskiya ta bayyana yanzu - Ganduje ya yi tsokaci kan nasarar da ya samu a kotu

Gaskiya ta bayyana yanzu - Ganduje ya yi tsokaci kan nasarar da ya samu a kotu

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi tsokaci kan gagarumar nasarar da ya samu yau a kotun kararrakin zaben jihar da aka yanke.

Ya siffanta wannan nasara a matsayin wata karin nasara ga al'ummar jihar Kano da suka yi zabe.

Sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki a ranar Laraba bayan sanarwan kotun zabe cewa ta yi watsi da karar PDP da Abba Kabir Yusuf.

Abba Anwar ya ruwaito gwamnan da cewa wannan shari'ar wata sabuwar nasara ce yayinda gaskiya ta bayyana, bayan an alantashi a matsayin zababben gwamnan jihar Kano bayan zagayen zabe na biyu a ranar 23 ga Maris.

Yace: "A lokacin da aka gudanar da zabe da muka samu nasara, yan hamayya Peoples Democratic Party, PDP, sun yanke shawarar cewa zasu kalubalanci nasararmu a kotu."

"Gashi ya bayyana karara cewa nasararmu gaskiyace, kamar yadda kotun ta tabbatar."

KU KARANTA: Jarumin maza: Ya bige masu garkuwa da mutane tare da sakin mutane da suka kama

Ganduje ya ce gwamnatinsa zata cigaba da samar da ayyukan cigaba ga jihar kamar yadda ta fara a wa'adin farko.

Ya mika godiyarsa ga al'ummar jihar da bashi daman jan ragamar mulkin jihar karo na biyu.

Ya tabbatarwa al'ummar jihar cewa ba zai nuna san kai wajen raba kayan cigaba da dukkan kananan hukumomin jihar 44 ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel