Yanzu Yanzu: Gwamna Yahaya ya zabi ‘yar Goje da wasu 17 a matsayin kwamishinoni

Yanzu Yanzu: Gwamna Yahaya ya zabi ‘yar Goje da wasu 17 a matsayin kwamishinoni

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya mika sunan Dr Husseina Goje, yar sanata Danjuma Goje a matsayin zababbiyar kwamishina tare da wasu 17 zuwa majalisar dokokin jihar.

A wata wasika wanda kakakin majalisar, Abubaka Sadiq Kurba, ya karanto a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba a lokacin zaman majalisar, surukin Sanata Goje, Ibrahim Dasuki Jalo Waziri wanda ya auri yayar Husseina ma na cikin wadanda aka zaba a matsayin kwamishina.

Sauran wadanda aka zaba sun hada da Dr Ahmad Gana; Dr Aishatu Usman Maigari; Barrister Zubairu Umar; Mohammed Magaji Gettado; Mr Julius Ishaya, Mrs Naomi Awak; Engineer Abubakar Bappa and Alhaji Muhammad Gambo Maigari.

Har ila yau an mika sunayen Malam Usman Jahun Biri; Alhaji Adamu Dishi; Alhaji Ibrahim Alhassan; Dr Habu Dahiru; Dauda Batari Zambuk; Mijinyawa Yahaya; Mela Audu Nunge; Meshak Lanco; Julius Ishaya and Mrs Naomi Joel Ishaya.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Dan Maina ya fito da bindiga domin hana a kama mahaifinsa - DSS

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa majalisar zata saki jadawalin tantance zababbun kwamishinonin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel