Jami'an kwastam sun kama buhunhunan tabar wiwi da darajarsu ya kai miliyan N169

Jami'an kwastam sun kama buhunhunan tabar wiwi da darajarsu ya kai miliyan N169

Jami'an hukumar Kwastam sun kama wata motar daukan kaya a jihar Osun makare da buhunhunan tabar wiwi da aka shigo da ita kasar nan ta iyakar Najeriya da ke garin Oke a jihar Ogun.

An boye buhunhunan tabar wiwi din a cikin dusar katako.

Da yake tabbatar da kama motar ga manema labarai a ranar Laraba, Zulkifli Abdullahi, shugaban ofishin hukumar Kwastam na yankin, ya ce jami'ansu sun kama motar da ta dauko ganyen tabar wiwi din a garin Elekokan da ke yankin karamar hukumar Iwajowa.

Abdullahi ya bayyana cewa wannan shine kamun ganyar tabar wiwi ma fi girma da jami'an hukumar Kwastam a yankin suka yi a 'yan kwanakin baya bayan nan.

Ya ce babban abin takaicin shine yadda jami'an Kwastam suka gaza samun damar kama direban motar da yaronsa, saboda, sun ruga da gudu cikin daji bayan sun hango motar jami'an Kwastam na nufo inda suke.

DUBA WANNAN: EFCC ta kama ma'aikatan hukumar INEC hudu a Zamfara, sunaye da hotunansu

A cewarsa, ya samu sahihan bayanan sirri a kan shigo da tabar wiwin daga kasar Ghana tun kafin a shiga da ita kasar Togo, sannan daga bisani a shiga da ita kasar Benin domin tsallako wa da ita zuwa Najeriya.

"Kamar yadda ku ke gani da idonku, akwai buhunhunan tabar wiwi guda 101 a boye a cikin motar. Mun san ana sayar da kowanne buhu a kan N120,000 Shekaru uku suka wuce, yanzu kuwa zai kai N150,000.

"Idan aka tara kudin tabar wiwi din a kan N120,000 kowanne buhu, kudinta zai kai miliyan N159,00, a takaice, darajar tabar wiwin zai kai miliyan N160. Allah ne kawai ya taimaki jami'an mu suka kama wannan kayan laifi. Allah ne kadai ya san irin illar da wannan ganyen tabar zai yi da an shiga da ita cikin kasa, ta fada hannun jama'a, musamman matasa masu tu'ammali da kayen maye," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel