Da dumi-dumi: Dan Maina ya fito da bindiga domin hana a kama mahaifinsa - DSS

Da dumi-dumi: Dan Maina ya fito da bindiga domin hana a kama mahaifinsa - DSS

Hukumar tsaro na sirri ta tabbatar da kamun Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar fansho.

Peter Afunanya, kakakin rundunar ya tabbatar da kamun a wani jawabi da ya saki a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba.

Yace an kama Maina ne a wani otel a Abuja a ranar 30 ga watan Satumba, 2019, cewa dansa yayi kokarin bude wuta akan jami’an DSS da suka aiwatar da aikin.

“Anyi kamun ne a otel din Pennsylvania Avenue, Utako, Abuja biyo bayan wata bukata ta EFCC na su taimaka wajen kama mai laifin” inji jawabin.

“An kama Maina tare da dansa mai shekara 20, Faisal Abdulrasheed Maina, wanda yayi kokarin hana kamun.

“Har ta kai yaron ya fito da bindiga domin hana jami’an aiwatar da aikinsu. Sai dai an kwace bindigar sannan aka kama shi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Obaseki ya sallami dukka hadimansa guda 264

"Ya kasance dalibin ajin karshe a jami’ar Kanada na Dubai inda yake karantar injiniya.”

A wani labari kuma, mun ji cewa hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta mika bukatar gurfanar da tsohon ministan aiyuka na musamman, Kabiru Turaki, akan zarginsa da take da damfarar naira biliyan 20 gaban babban kotun tarayya da ke Abuja.

Turaki, wanda ya shugabanci ma'aikatar aiyuka na musamman daga 2013 zuwa 2015 karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya fito takarar kujerar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP a 2019. Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ne ya yi nasara a kansa tun azaben fidda gwani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel