Yanzu-yanzu: Babban jami'in tsaron jami'iyyar APC, DSP Adamu ya rasu

Yanzu-yanzu: Babban jami'in tsaron jami'iyyar APC, DSP Adamu ya rasu

- Jam'iyyar APC ta sanar da rasuwar babban jami'in tsaron ta

- Marigayi Adamu ya yi aikin da rundunar 'yan sandan Najeriya na tsawon shekaru 35 kafin ya yi ritaya a 2006

- Anyi jana'izar marigayi Adamu a babban birnin tarayya, Abuja

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanar da rasuwar babban jami'in tsaron ta, DSP Adamu Aso (mai ritaya) wanda ya rasu a ranar Talata 1 ga watan Oktoban 2019 sakamakon mummunan hatsarin mota a Abuja.

Anyi jana'izar marigayin a babban birnin tarayya, Abuja kamar yadda sanarwar da sakataren yadda labarai na kasa na APC, Mallam Lanre Issa-Onilu ya fitar da ranar Laraba 2 ga watan Oktoba ta ce.

Issa-Onilu ya ce marigayin ya yi aiki da Rundunar 'yan sandan Najeriya na tsawon shekaru 35 kuma ya yi ritaya a 2006 yana matsayin mataimakin sufritandan 'yan sanda.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe 'Iblis' a jihar Ribas

"Ya yi aiki a matsayin mukadashin shugaban tsaro a sakatariyar jam'iyyar CPC na kasa, kafin daga baya jam'iyyar ta canja zuwa APC.

"Marigayi DSP Adamu Aso ya rasu ya bar mata da yara kuma dan asalin jihar Yobe ne.

"Jam'iyyar za tayi rashin kwarwarsa, dattaku da dabarun iya aikinsa," inji Issa-Onilu.

Ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan mamamcin da rundunar 'yan sandan Najeriya da kuma dukkan ma'aikatan jam'iyyar APC.

"Muna fata Allah ya bamu hakurin jure rashinsa," inji shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel