"Dimokradiyya ce ta yi nasara", Buhari ya yi magana a kan hukuncin kotun Kano da Filato

"Dimokradiyya ce ta yi nasara", Buhari ya yi magana a kan hukuncin kotun Kano da Filato

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya taya gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da takwaransa na jihar Filato, Simon Lalong, murnar samun nasara a kotun sauraron korafin zabe.

A hukuncin da suka yanke daban-daban a ranar Laraba, kotunan sauraron korafin zaben gwamna a Kano da Filato, sun tabbatar wa da gwamnonin na APC nasarar da suka samu a zaben da aka yi a cikin watan Maris.

Gwamnonin biyu na daga gwamnoni uku da zasu raka shugaba Buhari zuwa kasar Afrika ta kudu, shugaban kasar ya taya su murna ne a filin jirage na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja jim kadan kafin su tashi zuwa kasar Afrika ta kudu.

A wani jawabi da Malam Garba Shehu, kakakin shugaban kasa ya fitar, Buhari ya bayyana nasarar da gwamnoni suka samu a matsayin nasara ga dimokradiyya.

DUBA WANNAN: Cuta a shirin ciyar da dalibai: Jami'an DSS sun kama shugaban APC, wasu mutane biyu a Kano

Shugaba Buhari ya yaba wa mutanen Kano da na Filato bisa hakurin da suka nuna a lokacin da ake shari'ar da kuma barin bangaren shari'a ya yi aikinsa.

Kazalika, shugaba Buhari ya bukaci gwamnonin su hada kan jihohinsu tare da gudanar da mulki bisa doron inganta rayuwar 'yan Najeriya, kamar yadda yake a cikin manufar jam'iyyar APC da gwamnatin tarayya.

Buhari ya bawa gwamnoni tabbacin cigaba da samun goyon bayan gwamnatin tarayya wajen inganta tattalin arzikin jihohinsu, tsaro da muhalli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel