Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shilla kasar Afrika ta kudu tare da gwamnoni 3 da ministoci 7 (Hotuna)

Da ranan nan, shugaba Muhammadu Buhari ya tashi daga babbar filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja zuwa kasar Afrika ta kudu.

Mun kawo muku rahoton cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Afrika ta kudu a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba, 2019 kan al'amarin kin jin bakin fata da ke addabi kasar Afrika ta kudu a makonnin bayan.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan ne da ranan nan a jawabin da ya saki

.Shugaba Buhari zai tafi tare da gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano, gwamna Simon Lalong na Plateau da gwamna David Umahi na Ebonyi.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shilla kasar Afrika ta kudu tare da gwamnoni 3 da ministoci 7 (Hotuna)
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shilla kasar Afrika ta kudu tare da gwamnoni 3 da ministoci 7 (Hotuna)
Asali: Facebook

Daga cikin ministoci akwai ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama; ministan tsaro, Bashir Magashi; ministan lantarki, Saleh Mamman; ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola; da ministan ma'adinai, Olamilekan Adegbite.

Sauran ministocin sune ministan harkokin yan sanda, Maigari Dingyadi da karamar ministar masana'antu, kasuwanci da hannun jari, Mariam Katagum.

Hakazalika akwai NSA Babagana Munguno, dirakta janar na hukumar NIA, Ahmed Rufai da shugabar hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shilla kasar Afrika ta kudu tare da gwamnoni 3 da ministoci 7 (Hotuna)
Shugaba Buhari ya shilla kasar Afrika ta kudu
Asali: Facebook

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shilla kasar Afrika ta kudu tare da gwamnoni 3 da ministoci 7 (Hotuna)
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shilla kasar Afrika ta kudu tare da gwamnoni 3 da ministoci 7 (Hotuna)
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel