Yanzu Yanzu: Obaseki ya sallami dukka hadimansa guda 264

Yanzu Yanzu: Obaseki ya sallami dukka hadimansa guda 264

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya sallami dukkanin hadimansa guda 264 da ke wakiltan unguwanni da kananan hukumomi a jihar.

Hadiman da aka kora a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba, sun hada da hadimai na musamman guda 193, manyan hadimai na musamman guda 54 da hadimai na musamman guda 18, jaridar The Nation ta ruwaito.

Osarodion Ogie, sakataren jihar ya tabbatar da lamarin, inda yace sallaman na daga cikin shirin Gwamna Obaseki na yin garambawul a gwamnatin domin isar da aiki mai inganci.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa (hotuna)

Ogie ya bayyana cewa za a sanar da sabbin nade-nade cikin kwanaki 30 masu zuwa.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta mika godiyarta ga hadiman da aka sallama akan gudunmawar da suka ba jihar da kuma tabbacin cigaba da alaka mai kyau a shekaru masu zuwa.

Yace: “Ana umurtansu da su mika dukkanin kayayyakin gwamnati da takardun zuwa ga ofishin sakataren jihar.”

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa (hotuna)

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole, ya karyata ikirarin gaba tsakaninsa da Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel