Dalilin da yasa kotun sauraron korafin zabe ta kori karar Abba a Kano

Dalilin da yasa kotun sauraron korafin zabe ta kori karar Abba a Kano

A ranar Laraba ne kotun sauraron korafin zaben gwamnan jihar Kano da ke zamanta a unguwar Bompai ta tabbatar da sake samun nasarar gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a watan Maris.

Jam'iyyar PDP da dan takararta na gwamna a jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, sun garzaya kotu domin neman ta kwace kujerar gwamnan jihar Kano daga hannun Ganduje tare da mika ta gare su bisa hujjar cewa sune suka lashe zaben a zahirin gaskiya, amma aka murde musu.

Da take zartar da hukunci a ranar Laraba, babbar alkaliyar kotun, Jastis Halima Shamaki, ta ce kotun ta yi watsi da bukatar Abba da PDP ne saboda sun gaza tabbatar da ikirarin da suka yi na cewa an tafka musu magudi a zaben gwamnan.

Jastis Shamaki ta kara da cewa jam'iyyar PDP da dan takarar ta na iya daukaka kara idan basu gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba.

Kazalika, ta ja kunnen magoya bayan 'yan takarar da jam'iyyunsu da su guji tayar da rikici tare da bayyana cewa Kano jihar ta ce ita ma.

DUBA WANNAN: EFCC ta kama ma'aikatan hukumar INEC hudu a Zamfara, sunayensu da hotuna

A yayin da magoya bayan gwamna Ganduje ke nuna farincikinsu da wannan hukunci na kotu, magoya bayan Kwankwasiyya sun nuna rashin jin dadinsu.

Ganduje ya samu nasarar lashe zaben kujerar gwamnan jihar Kano ne bayan an yi zabe karo na biyu, wanda ake kira da 'raba gardama'. Bayan an maimaita zaben a karo na biyu a wasu mazabu, Ganduje ya samu kuri'u 45,876 yayin da Abba ya samu kuri'u 10,239.

A jimillar sakamakon zabe na farko da na biyu, Ganduje ya samu kuri'u 1,033,695, yayin da Abba ya samu kuri'u 1,024,713. Sakamakon zaben ya nuna cewa Ganduje lashe zaben da tazarar kuri'u 8,982.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel