Da duminsa: Kotun sauraron korafin zaben gwamnan a jihar Filato ta yanke hukunci

Da duminsa: Kotun sauraron korafin zaben gwamnan a jihar Filato ta yanke hukunci

Kotun sauraron korafin zaben gwamnan jihar Filato da ke zamanta a Jos ta tabbatar da sake samun nasarar gwamnan jihar, Simon Lalong, a zaben da aka gudanar a watan Maris, kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta fara sanar wa.

Jam'iyyar PDP da dan takarar ta na gwamna a jihar, Jeremiah Useni, sun garzaya gaban kotun sauraron zabe domin neman ta soke zaben gwamna Lalon bisa zargin cewa an tafka musu magudi yayin zaben.

Tun kafin kotun ta zartar da da hukunci, Legit.ng ta wallafa cewa dararuruwan magoya bayan dan takarar gwamnan APC a shekarar 2019 a jihar Plateau, Mista Simon Lalong da babban abokin hammayarsa Sanata Jeremiah Useni na jam'iyyar PDP a ranar Laraba sun mamaye harabar kotun sauraron karrarakin zaben jihar da ke Jos inda Mai shari'a H.A. Saleeman ke jagorantar wasu lauyoyi da za su yanke hukunci kan zaben.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa kotun sauraron korafin zabe ta kori karar Abba a Kano

Useni ya shigar da karar kallubalantar nasarar da Lalong ya yi na yin tazarce a jihar inda ya yi ikirarin cewa an soke kuri'u a bangarorin da PDP ke da rinjaye kana ya kuma yi ikirarin cewa Lalong bai cancanta ya tsaya zabe ba.

Magoya bayan 'yan takarar biyu sanye da riguna masu dauke da alamar wadanda suke goyon baya sun sha alwashin cewa ba za su bar harabar kotun ba har sai an yanke hukunci.

An aike da tawagar 'yan sanda daga hedkwatan rundunar ta Jos domin tabbatar da cewa babu wani barkewar rikici ko saba doka da oda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel