Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa (hotuna)

Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa (hotuna)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba, ya jagoranci zaman majalisar zartarwa da ake yi a kowani mako.

An fara zaman majalisar ne misalin karfe 11 na safe a fadar shugaban kasar, Abuja.

Daga cikin wadanda suka halarci zaman majlisan harda mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Sauran sun hada da babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, da kuma mukaddashin shugaban ma’aikatan tarayya, Folasade Yemi-Esan.

Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa (hotuna)
Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa
Asali: Facebook

A karshen zaman, ana sanya ran Shugaban kasa Buhari zai kai ziyarar kwanaki uku a Afirka ta Kudu.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta ce dan jam'iyyar APC da yayi karar Tambuwal a kotun zabe yana da gaskiya

Shugaba Buhari zai kai ziyarar ne bisa bukatar shugaban kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, domin tattauna wa a kan hare-haren da aka dinga kai wa bakin haure, musamman Najeriya, a kasar.

Gwamnoni uku da ministoci bakwai da wasu hadimai uku ne zasu raka shugaban Buhari zuwa kasar Afrika ta Kudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel