Shari'ar gwamnan Plateau: Magoya bayan Lalong da Useni sun mamaye kotu suna jiran sakamako

Shari'ar gwamnan Plateau: Magoya bayan Lalong da Useni sun mamaye kotu suna jiran sakamako

Daruruwan magoya bayan dan takarar gwamnan APC a shekarar 2019 a jihar Plateau, Mista Simon Lalong da babban abokin hammayarsa Sanata Jeremiah Useni na jam'iyyar PDP a ranar Laraba sun mamaye harabar kotun sauraron karrarakin zaben jihar da ke Jos inda Mai shari'a H.A. Saleeman ke jagorantar wasu lauyoyi da za su yanke hukunci kan zaben.

Useni ya shigar da karar kallubalantar nasarar da Lalong ya yi na yin tazarce a jihar inda ya yi ikirarin cewa an soke kuri'u a bangarorin da PDP ke da rinjaye kana ya kuma yi ikirarin cewa Lalong bai cancanta ya tsaya zabe ba.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe hatsabibin mai garkuwa da mutane 'Iblis'

Magoya bayan 'yan takarar biyu sanye da riguna masu dauke da alamar wadanda suke goyon baya sun sha alwashin cewa ba za su bar harabar kotun ba har sai an yanke hukunci.

An aike da tawagar 'yan sanda daga hedkwatan rundunar ta Jos domin tabbatar da cewa babu wani barkewar rikici ko saba doka da oda.

Ku biyo mu domin karin bayani...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel