Tirkashi: 'Yan bindiga sun kashe wani dan majalisa

Tirkashi: 'Yan bindiga sun kashe wani dan majalisa

- 'Yan bindiga da ake zargin makasan haya ne sun harbe wani dan majalisa a jihar Delta

- Dan majalisar mai suna Venture Kagbude, ya dawo daga duba gini da yake wa mahaifiyarsa ne a yankin Okuoke

- Dan majalisar wanda basarake ne, ya kasance shugaban kungiyar Okirighre a karamar hukumar Sapele kafin rasuwarsa

'Yan bindiga sun kashe dan majalisa, Venture Kagbude a karamar hukumar Sapele ta jihar Delta.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, ana zargin hayar 'yan bindigar hayarsu aka yi don kashe dan majalisar inda kuwa suka kashesa a ranar Talata, 1 ga watan Oktoba, 2019 akan titin Warri.

KU KARANTA: Mata 5 da suka fi kasaita a Najeriya

Dan majalisar wanda kuma sarkin gargajiya ne, ya kasance shugaban kungiyar Okirighre a karamar hukumar Sapele ta jihar Delta.

Kamar yadda majiyarmu ta sanar, "Marigayin, Venture, na dawowa daga yankin Okuoke da ke titin Sapele-Effurun zuwa Warri inda ya je duba gidan da yake ginawa mahaifiyarsa ne 'yan bindigar suka harbeshi."

Jaridar Punch ta gano cewa, lamarin ya auku ne wajen karfe 6:00 na yammacin ranar Talata.

Lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun 'yan sandan, Onome Onowakpoyeya, ta ce zata kira wakilin Punch don bada bayanin aukuwar lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel