Gwamnan jihar Katsina ta karbi mutane 23 da aka siyar don bauta a kasar Burkina Faso

Gwamnan jihar Katsina ta karbi mutane 23 da aka siyar don bauta a kasar Burkina Faso

- A daren ranar Talata ne gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya karbi mutane 223 na jihar da aka siyar don bauta a kasar Burkina Faso

- Daga cikin mutanen 23 akwai 13 maza daga karamar hukumar Kankara ta jihar, sai 10 'yan jihar Zamfara

- Gwamnan ya bayyana cewa a shirye gwamnatinsa take don karbo duk dan jihar da ke fuskantar halin tozarci a wata kasa

A daren Talata ne gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya karbi mutane 23 da masu garkuwa da mutane suka siyar a kasar Burkina Faso a matsayin bayi.

Mutanen sun hada da maza 13 daga karamar hukumar Kankara ta jihar inda sauran mazan 10 asalin 'yan jihar Zamfara ne.

A baya ma an taimaki mutane 7 sun dawo gida daga kasar Burkina Faso din.

Wani Alhaji Usman daga karamar hukumar Kankara ne ya siyarda mutanen ga wata mata mai safarar mutane dake Jamhuriyar Benin.

KU KARANTA: Wata sabuwa: EFCC ta bukaci karbar kadarorin wani tsohon minista

Daga baya matar ta siyarda su ga wani mai safarar mutane a kasar Burkina Faso.

Daya daga cikin wadanda ibtila'in ya fada kansa mai suna Ali Ali, ya ce an yi musu alkawarin aiyukan yi ne a kasar Burkina Faso.

Ali ya bayyana cewa, an kwashesu ne daga karamar hukumar kankara ne tare da suaran 'yan uwansa ind aka mikasu ga wata mata a kasar jamhuriyar Benin wacce daga baya ta mikasu ga wani mutum a kasar Burkina Faso.

Ya kara da bayyana yadda ake tozartasu da wulakantasu. ya kara da cewa, wadanda basu da lafiya a cikinsu an hana su magani ko kaisu asibiti; abinda yasa ya zargi cewa ko an siyar da su ne.

Gwamna Masari da ya yi jawabi yayin karbar mutanen, mutane biyu daga cikin wadanda aka dawo dasu gidan sun ki dawowa sakamakon zarginsu da ake da hannu a cikin lamarin.

Ya yi alkawarin cewa, gwamnati a shirye take da dawo da duk wand yake cikin irin wannan halin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel