Kotu ta ba Ganduje da APC nasara a zaben Gwamnan Jihar Kano

Kotu ta ba Ganduje da APC nasara a zaben Gwamnan Jihar Kano

Shari’ar da ake yi tsakanin jam’iyyar APC mai mulki da kuma PDP mai adawa ta zo karshe a kotun farko da ke sauraron korafin zaben bayan da Alkali ta yi watsi da karar da PDP ta shigar.

Kotu ta tabbatar da nasarar da Abdullahi Ganduje a zaben gwamnan jihar Kano da aka yi a watan Maris. Hakan na zuwa ne bayan ‘dan takarar PDP, Abba Kabir Yusuf ya kalubalanci nasarar APC.

Mai shari’a Halima Shamaki Muhammad ce shugaban Alkalan da ke sauraron wannan kara kuma ta yi fatali da korafin da jam’iyyar PDP ta kawo gabanta a zaman karshen da ta yi yau Laraba.

Kotu ta yanke wannan hukunci ne kamar yadda ta tanada a Ranar 2 ga Watan Oktoba bayan kusan watanni shida ana sauraron karar. Alkalin ta tabbatar da cewa APC ce ta lashe zaben Kano.

KU KARANTA: Yadda Jami'an tsaro su ka karade Kano saboda zaman shari'ar karshe

Daya daga cikin Hadiman gwamnan na Kano, Salihu Tanko Yakassai ya tabbatar da wannan inda ya fito shafinsa na Tuwita yana taya Maigidan na sa murnar wannan sabuwar nasara da ya samu.

Yakassai yake cewa: "Tsarin bada ilmi tilas kuma kyauta ya samu gindin zama a Kano da wannan hukunci na kotu. Mai ba gwamnan shawara ya bayyana wannan ne a shafinsa na @Dawisu.

“Nasarar mu a kotun zabe ya tabbatar da cewa duk da irin suka da wulakanci daga wasu tsirarru, idan Ubangiji ya na bayanka, to babu abin da wani zai iya, kuma nasara za ta tabbata.” Inji sa.

Yanzu haka dai jami’an tsaro sun cika jihar Kano domin kwantar da tarzoma idan ta tashi. Rahotanni kuma na yawo cewa gwamna mai-ci Abdullahi Ganduje ba ya kasar a wannan lokaci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel