Akwai bukatar hadin-kai don a ci zaben Kogi - Atiku ya fadawa Wada da Dino

Akwai bukatar hadin-kai don a ci zaben Kogi - Atiku ya fadawa Wada da Dino

Yayin da ake shiryawa zaben gwamna a jihar Kogi, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma ‘dan takarar adawa a zaben shugaban kasa na bana ya sa baki a cikin rikicin jam’iyyar PDP.

Kamar yadda rahotanni su ka zo mana yau, Laraba 2 ga Watan Oktoban 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya fara kokarin sasanata ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP da su ke fushi da jam’iyyar adawar.

A yunkurin da Atiku Abubakar ya ke yi na ganin PDP ta dinke har ta samu nasara a zaben gwamnan Kogi da za a yi a Watan Nuwamba, ya gana da Mohammed Wada da kuma Dino Melaye.

Atiku ya yi wannan ganawa da ‘dan takarar gwamnan na PDP wanda ya samu tikiti cikin rikici a Birnin Dubai. Haka zalika Atiku ya tattauna da Sanata Dino Melaye wanda ya rasa tutar jam’iyya.

Kamar yadda majiyar This Day ta bayyana, Atiku ya sa baki a rigimar ne bayan Sanata Dino Melaye ya yi jifa da tayin da aka yi masa na jagorantar yakin neman zaben PDP a jihar ta Kogi.

‘Dan takarar gwamnan na PDP, Mohammed Wada ne ya yi kokarin tuntubar Atiku Abubakar domin ganin ya dinke masu duk wata baraka da ta bijirowa jam’iyyar bayan zaben tsaida gwani.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun cika gari yayin da ake shirin jin sakamakon zaben Kano

Babban ‘Dan siyasar ya fadawa Jiga-jigan PDP na jihar Kogi cewa dole su hada-kai a gida idan har su na son ganin sun samu nasara a zaben da za a yi inda za su gwabza da gwamnan APC.

Jinkirin da aka samu wajen wannan sulhu ne ya sa PDP ba ta soma yawon kamfe na zaben da za a yi a cikin Watan Nuwamban nan ba. Babu mamaki ‘Ya ‘yan jam’iyyar su janye kara da ke kotu.

Nan gaba kadan ana sa ran Atiku zai gana da tsohon gwamnan Kogi Ibrahim Idris da ‘Dansa watau Sulaiman wanda ake zargin cewa shi ne kashin bayan takarar Mohammed Wada a yanzu.

Wani abin sarkarkiya shi ne tsohon gwamnan da ya mulki Jihar Kogi daga 2003 har zuwa 2011 yana rikici ne da ‘Dansa da Mahaifiyarsa a dalilin mara bayansu ga ‘dan takarar da bai tare da shi.

Iyalin tsohon gwamnan sun yi haka ne domin rama abin da Mahaifinsu ya taba yi masu a baya. Abin da ake so Atiku ya yi shi ne ya sa Idris Wada ya janye karar da ya kai Surukinsa gaban kotu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel