Zaben gwamnan Kano: An baza 'yan sanda 3,000 yayin da kotu ke shirin yanke hukunci

Zaben gwamnan Kano: An baza 'yan sanda 3,000 yayin da kotu ke shirin yanke hukunci

- An kammala shirin zartar da hukuncin kan zaben gwamnan jihar Kano

- Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta aike da 3,000 domin inganta tsaro a jihar

- Kakakin rundunar 'yan sanda, DSP Abdullahi Haruna ya ce an bawa dukkan sassan 'yan sandan umurnin su kasance cikin ko ta kwana

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta baza jami'an tsaro 3,000 a jihar gabanin yanke hukuncin zaben gwamnan jihar da kotun sauraron karrakin zabe na jihar za ta yanke a yau Laraba 2 ga watan Oktoba.

The Guardian ta ruwaito cewa al'ummar Kano na cikin zullumi a ranar Talata 1 ga watan Oktoba yayin da ake ta kaiwa da komowa a gidan gwamnati da ke Miller Road hedkwatan Kwankwasiyya na jihar.

A cewar rahoton, an girke jami'an tsaro dauke da makamai a wurare daban-daban da suka da Murtala Mohammed Way, Hadiejia Road, Ahmadu Bello Road, Statre road da wasu manyan tituna a jihar.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe hatsabibin mai garkuwa da mutane 'Iblis'

A yayin da ya ke tabbatar da tsaurara tsaro a jihar cikin wata hirar tarho, Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi ya ce an bawa dukkan 'yan sandan jihar umurnin su kasance cikin shiri.

Haruna ya ce har yanzu dokar hana taron siyasa da wasu tarukkan da aka kafa a jihar yana nan har yanzu yana aiki. Ya yi gargadin cewa ba za a amince da duk wani halin rashin da'a ba yayin da kotun ke zaman ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel