Da duminsa: Barayi sun kai hari majalisar dokokin jiha

Da duminsa: Barayi sun kai hari majalisar dokokin jiha

Wasu barayi sun kai hari majalisar dokokin jihar Oyo inda sukayi awon gaba da wayoyin wuta na kimanin N500,000.00, kakakin majalisa, Kemi Ojoawo, ta bayyana hakan a ranar Laraba.

A cewarta, yan fashin sun fasa cikin majalisar ne a daren Alhamis da ya gabata kuma suka tafka sata.

Hakan ya kawo cibaya wajen gudanar da ayyukan yan majalisar jihar a wannan makon.

Wani majiya wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa wannan ba shi bane karo na farko da ake tafka sata a majalisar ba.

Ya ce tun kafin yanzu ana satan wayoyin wutan lantarki, fankoki, na'urorin komfuta da sauransu a majalisar dokokin jihar.

KU KARANTA: Ba zan nemi yin tazarce ba - Buhari

Yace: "Wannan shine karo na uku da za'ayi sata cikin dare. Duk da cewa wannan shine karo na farko a majalisa ta 9, amma na tuna sarai cewa a majalisar da ta shude, sau biyu ana tafka sata kuma sai da aka kashe mimanin milyan daya wajen gyara."

"Abin takaicin shine duk da binciken da aka gudanar, babu wanda aka kama har yanzu. Shi yasa abin ke cigaba da faruwa."

Kakakin majalisa, Kemi Ojoawo, ta bayyanawa manema labarai cewa majalisar na gudanar da bincike kan fashin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel