An ceto bayi 23 daga kasar Burkina Faso zuwa Katsina

An ceto bayi 23 daga kasar Burkina Faso zuwa Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta ceto mutane 23 da aka mayar bayi ta karfin tsiya a kasar Burkina Faso.

Gwamnan jihar, Alhaji Aminu Bello Masari, ya karbi wannan mutane 23 a daren ranar Talata cikin birnin Katsinan Dikko, bayan da jami'an gwamnatin jihar suka dawo dasu gida daga kasar Burkina Faso.

Masari yayin gabatar da jawabai ga manema labarai ya yi bayanin cewa, wani dillalin bayi ne, Alhaji Usman, ya jefa mutanen 23 cikin halin ni 'ya su bayan yaudarar su da ikirarin nema masu hanyar samu mai tsoka a kasashen ketare, inda a karshe ya sayar da su ga wata mata mai sayan bayi a kasar jamhuriyyar Benin.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, cikin mutanen 23, 13 sun kasance 'yan asalin karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina yayin da sauran goman suka kasance 'yan asalin jihar Zamfara.

KARANTA KUMA: Kasafin Kudin 2020: Buhari zai jagoranci zaman majalisar tattalin arziki na musamman a ranar Asabar

Ana iya tuna cewa a watan Nuwamban 2017 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin ganawa da 'yan Najeriya mazauna kasar Ivory Coast a birnin Abidjan, ya bayyana bacin ransa da cewa ana sayar da 'yan kasar nan tamkar awaki a Libya.

Hakazalika a shekarar 2017 ne wasu 'yan Najeriya suka gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Libya da ke birnin Abuja, inda suka nuna bacin ransu game da tozartawar da ake yi wa bakaken fata ciki har da 'yan Najeriya a kasar Libya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel