Kasafin Kudin 2020: Buhari zai jagoranci zaman majalisar tattalin arziki na musamman a ranar Asabar

Kasafin Kudin 2020: Buhari zai jagoranci zaman majalisar tattalin arziki na musamman a ranar Asabar

Dangane da gabatar da kasafin kudin kasa na 2020 a mako mai zuwa a gaban majalisar tarayya, shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai jagoranci wani zaman majalisar tattalin arziki na musamman a ranar Asabar.

Wannan rahoto na kunshe ne cikin sanarwar da wani babban jami'in gwamnati ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, gwamnatin tarayya na yunkurin kafa wani sabon tsari na dawo da kasafin kudin kasar daga tsakanin watan Mayu/Yuni zuwa Janairu/Dasumba.

Zaman majalisar tattalin arzikin da shugaban kasa Buhari zai jagoranta a ranar Asabar zai tattauna dangane da shirye-shiryen gabatar da kasafin kudin Najeriya na 2020 a gaban majalisun tarayya biyu na kasar.

A makon da ya gabata ne cikin watan Satumba, ya kamata a gabatar da kasafin kudin kasa, inda aka samu jinkiri a sanadiyar shugaban kasa Buhari da ya halarci taron majalisar dinkin duniya da aka gudanar a birnin New York na kasar Amurka.

KARANTA KUMA: Za'a fara karbar kuɗin fito a dukkanin manyan hanyoyin Najeriya - Fashola

Bayan jagorantar zaman majalisar zartarwa a yau Laraba, shugaba Buhari ya kuma shilla kasar Afirka ta Kudu tare da gwamnoni 3 da kuma ministoci 7, domin ganawa da takwaransa, Cyril Ramaphosa, a kan takaddamar kin jinin baki da ake yi kasar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel