Za'a fara karbar kuɗin fito a dukkanin manyan hanyoyin Najeriya - Fashola

Za'a fara karbar kuɗin fito a dukkanin manyan hanyoyin Najeriya - Fashola

Ministan ayyuka da gidaje, Mista Babatunde Raji Fashole, a ranar Laraba 2 ga watan Oktoba, ya zayyana shirin gwamnatin tarayya na sake dawo da wata tsohuwar hanyar karbar haraji a hannun matafiya.

Fashola ya ce tuni shirye-shirye sun kan kama dangane da aiwatar da kudirin gwamnatin tarayya na dawo da tsarin karbar kuɗin fito a manyan hanyoyin kasar.

Ministan ya ce kirin ya rage gwamnatin tarayya ta kaddamar da wannan sabon tsari na karbar haraji a hannun direbobin mota masu cin moriyar manyan hayoyi a kasar.

Jaridar Vanguard ta ambato furucin ministan a yayin da yake ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa, bayan zaman majalisar zartarwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a Larabar yau.

KARANTA KUMA: Remi Duyile: Haifaffiyar Najeriya ta zama kwamishina a kasar Amurka

Ya ce babu wani dalili da zai hana sake bijiro da wannan tsohon tsari domin kuwa doka gami da kundin tsarin mulkin kasa sun halasta karbar kuɗin fito a Najeriya.

Kamar yadda tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana, ya zuwa abin da ya rage cikin shirin bai wuce kirdadon Bankunan kasar nan ba da su kammala kafa hanyoyin karbar kuɗin fito a hannun direbobin manyan hanyoyi ba tare da sun biya kai tsaye ba da nau'ikan kudi na tsaba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel