Kotu ta ce dan jam'iyyar APC da yayi karar Tambuwal a kotun zabe yana da gaskiya

Kotu ta ce dan jam'iyyar APC da yayi karar Tambuwal a kotun zabe yana da gaskiya

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Sokoto a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba, ta kaddamar da cewar karar da Ahmed Aliyu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya shigar inda yake kalubalantar sanar da Gwamna Aminu Tambuwal a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna na da inganci sannan kuma ya dace a doka.

Kotun zaben yayinda take yanke hukunci akan kin yarda da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da Gwamna Tambuwal suka nuna kan kara inda suka bukaci a kori kara saboda rashin inganci, tayi watsi da korafin nasu inda ta bayyana cewa an shigar da karar yadda ya kamata.

Kotun zaben ta kuma kara da cewa masu karar sun biya kudin da ya kamata domin shigar da karar.

Ta zartar da hukunci sabanin korafin wadanda ake kara inda ta bayyana cewa an shigar da karar yadda ya kamata sannan masu karar sun sanya hannu daidai. Ta kuma kara da cewa rashin shiga abokin takarar masu karar bai isa hujjar da za a mayar da karar mara inganci ba.

Akan dukka lamarin jagoran kotun zaben, Justis Abbas Bawale ya zartar da cewa bukatar wadanda ake kara da ke neman a kori karar bai da fa’ida sannan kuma cewa bata lokacin shari’a ne.

KU KARANTA KUMA: Abba ko Ganduje?: Kotun sauraron korafin zaben gwamna ta fara yanke hukunci

A halin da ake ciuki, kotun shari'ar zaben ta jihar Sokoto na zama ne a unguwar Wuse da ke birnin Abuja. An dai mayar da zaman sauraron karar zuwa Abuja saboda yanayin da jihar take ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel