Remi Duyile: Haifaffiyar Najeriya ta zama kwamishina a kasar Amurka

Remi Duyile: Haifaffiyar Najeriya ta zama kwamishina a kasar Amurka

  • 'Yar Najeriya, Remi Duyile, ta zama kwamishina ta gundumar Prince George a kasar Amurka
  • Lauyan koli ya jihar, Aisha Braveboy, ta rantsar da Duyile a ranar 23 ga watan Satumban da ya gabata
  • Sabuwar Kwamishinan ta ma'aikatar al'adu ta kasance tsohuwar shugaba ta Bankin Amurka

A ranar Litinin 23 ga watan Satumban da ya gabata ne aka rantsar da haifaffiyar Najeriya, Remi Duyile, a matsayin kwamishina ta farko a kasar Amurka da ta fito daga nahiyyar Afirka.

An rantsar da Duyile ne a matsayin kwamishinan ma'aikatar kula da harkokin al'adu kamar yadda ta bayyana a shafin zauren sada zumunta na Instagram.

Duyile ta wallafa wani hoto a shafinta na zauren sada zumunta, inda ta nuna farin cikin karbar rantsuwa daga lauyar koli, Aisha Braveboy, a matsayin kwamishinan ma'aikatar kula da harkokin al'adu ta gundumar Prince George a jihar Maryland ta kasar Amurka.

Duyile ta kasance tsohuwar shugaba ta Bankin Amurka, bayan shafe tsawon shekaru 17 tana aiki da Bankin wanda ta fara tun daga karamar ma'aikaciya zuwa mataimakiyar shugaba gabanin ta haye madafarsa ta iko.

A bangaren ilimi kuma, Duyile wadda ta kasance 'yar asalin jihar Ondon Najeriya, ta yi karatun digiri na farko a fannin harkokin kasuwanci, inda kuma tayi na biyu a fannin tsimi da tanadi daga jami'ar District of Columbia ta kasar Amurka a tsakanin shekarar 1982 zuwa 1987.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa za ta hada kai da hukumomin tsaro domin magance ta'adar garkuwa da mutane

Idan ba'a manta ba jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, an nada wasu 'yan Najeriya hudu a cikin kwamitin shawarwari kan harkokin 'yan Afirka mazauna kasashen ketare a gundumar Prince George.

Jerin 'yan kwamitin wanda Vincent Iweanoge dan Najeriya ke jagoranta sun hadar da; Dr Anu Esuola (Najeriya); Koby Sarconi (Ghana); Dr Joy Davis (Najeriya); Kevin Nyona (Kenya); Sylvia Dasi (Kamaru); Dr Angela Essamuah (Uganda); da kuma Victor Ogbonna (Najeriya).

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel