Majalisar Dattawa za ta hada kai da hukumomin tsaro domin magance ta'adar garkuwa da mutane

Majalisar Dattawa za ta hada kai da hukumomin tsaro domin magance ta'adar garkuwa da mutane

A yayin da ta'adar masu garkuwa da mutane ta zamto ruwan dare tare da ci gaba da ta'azzara a fadin Najeriya, Majalisar Dattawa yayin zaman da ta gudanar a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba, ta bijiro da wasu matakai domin magance wannan mummunar barazana da ta yi wa kasar nan dabai-bayi.

Wannan mataki da majalisar ta yi kudirin dauka na zuwa ne a yayin da wasu manyan sanatoci musamman Dino Melaye, Eyinnaya Abaribe da kuma Muhammad Danjuma Goje suka ba da sharwari a madadin 'yan Najeriya domin agazawa hukumomin tsaro fatattakar alakakai na ta'adar masu garkuwa.

Sanatocin sun yi babatu dangane da rashin ingataccen tsaro a wasu manyan hanyoyin kasar, inda suka bai wa hukumomin tsaro shawarar amfani da fasahu na zamani domin tankado keyar wadanda ke nufin kasar nan da sharri.

Dalla Dalla ga dai yadda shawarwarin majalisar dattawan suka kasance

1. Samar da kariya tare da managarcin tsaro a babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja da kuma sauran manyan hanyoyi na kasar.

2. A ja kunnen sufeto janar na 'yan sanda Muhammadu Adamu, da ya kara zage dantsensa wajen tsare rayuka da dukiyoyin al'ummar Najeriya.

3. Neman hukumomin tsaro da su rinka amfani da na'urori da kayayyaki na fasahar zamani wajen bankado miyagun ababe masu nufin kasar da sharri.

4. Hukumar kula da shige da fice da kuma sauran takwarorinta su zage dantse wajen kula da iyakokin kasar domin dakile shigowar bakin haure ta hanyar da ta saba wa ka'ida.

5. Majalisar Tarayya tayi kyakkyawan tanadi domin mallaka wa hukumomin tsaro ingatattun makamai.

6. Majalisar Dattawa ta bijiro da tsauraran matakai da dokoki na hukunta masu ta'adar garkuwa da mutane.

7. A yi riko hannu biyu- biyu tare da karbar dukkanin shawarwari da kwamitin majalisar a kan kula da harkokin tsaron kasa ya gabatar.

A wani rahoto mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, wasu matafiya sun yi gamo da ajali bayan da suka afka tarkon masu ta'adar garkuwa da mutane a babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja, yayin dawowarsu daga birnin Fatakwal na jihar Ribas.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel