Babu abin da ke tsakani na da Buhari face biyayya sau da kafa - Osinbajo

Babu abin da ke tsakani na da Buhari face biyayya sau da kafa - Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinabjo ya ce babu abin da ke tsakaninsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari face biyayya sau da kafa

- Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne cikin wani sakon taya murnar zagoyar ranar samun 'yanci da Najeriya tayi a ranar Talata, 1 ga watan Oktoba

- Osinbajo bayan shan alwashin ci gaba da yi wa shugaban kasa Buhari biyayya sau da kafa, ya ce bai taba cin karo da magarcin ubangida ba kamar sa

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi watsi da rade-radin da ke yaduwa na zargin zaman doya da manja da ke tsakanin sa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, lamarin da ya ce kanzon kurege ne da shaci fadi da ke kai komo musamman a zaurukan sada zumunta.

Farfesa Osinbajo yayin kawar da shakku da yi wa 'yan adawa raddi, ya ce babu abin da ke tsakanin sa da shugaban kasa Buhari face biyayya sau da kafa da kuma yi wa juna kyakkyawan fata nagari.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, wannan sako na kunshe ne cikin wata mujalla mai sunan "This is Nigeria" wato "Wannan ce Najeriya" da aka rarraba yayin murnar zagoyar ranar samun 'yan kan Najeriya a jiya Talata 1 ga watan Oktoba a wata liyafar dare da aka gudanar a dakin taro na Banquet Hall da ke fadar shugaban kasa a birnin Abuja.

A shafi na 15 cikin wannan mujalla, wani sako na Osinbajo baya ga bayyana murnar da farin cikin cikar Najeriya shekaru 59 da samun 'yancin kai daga hannun Turawan mulkin mallaka na Birtaniya, ya kuma jaddada goyon baya gami sa biyayya sau da kafa ga shugaban kasa Buhari.

Cikin sakon da ya bayyana a mujallar, Osinbajo ya taya shugaban kasa Buhari murnar samun 'yanci da kuma Ahmed Bola Tinubu a matsayin babban mai fada a ji na kasa, sai kuma Dr. Aisha Muhammadu Buhari, uwargidan shugaban kasa a matsayin uwa ga dukkanin al'ummar kasar nan baki daya.

Mataimakin shugaban kasar ya kuma sake jaddada cewa Buhari sai sauke nauyin dukkanin alkawurran da ya dauka, inda ya misalta shi a matsayin magarcin ubangida mafi soyuwa da ya taba aiki a karkashin sa.

Ana iya tuna cewa makonni kadan da suka gabata ne shugaban kasa Buhari ya kaddamar da majalisar bai wa shugaban kasa shawara kan tattalin arziki biyo bayan rushe kwamitin tattalin arzikin kasar, wanda mataimakin shugaban kasa Osinbajo ke jagoranta.

Sanadiyar haka wata kungiya ta shugabannin Kudu da kuma yankin tsakiyar Najeriya, SMBLF, a ranar Lahadin da ta gabata ta kaddamar ta cewa, tabbas akwai babbar damuwa a ofishin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, biyo bayan takaddamar da ta kunno kai dangane da ofishin nasa kwanaki kadan da suka gabata.

KARANTA KUMA: Jihar Akwa Ibom ta fi kowace jiha kwazo a Kudancin Kudu - Bankin Duniya

A sanadiyar haka kungiyar ta bukaci fadar shugaban kasa da ta fito karara ta bayyana abin da ta ke nufi a kan mataimakin shugaban kasar ko kuma ta gaggauta mayar masa da karfin ikon da a baya ya rataya a wuyansa.

Wannan bukata na zuwa ne a yayin da shugabannin kungiyar suka fidda wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai a birnin Ikko na jihar Legas, inda suka ce rage wa mataimakin shugaban kasa karfin iko a kasar na wasu nauye-nauye wanda a baya suka rataya a wuyansa na cin karo da ambaton gwamnonin jam'iyyar APC wanda suka ce babu wani zaman doya da manja da ake yi a fadar shugaban kasa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel