Idan majalisa tace sauya fasalin lamura ne mafita, Buhari zai aiwatar da hakan – Garba Shehu

Idan majalisa tace sauya fasalin lamura ne mafita, Buhari zai aiwatar da hakan – Garba Shehu

Kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mallam Garba Shehu yayi bayani akan yanda gwamnati zata yi shirye-shirye kan sake sauya fasalin lamuran kasa.

Yayin da ake cigaba da tattauna lamarin inda wasu da dama suka nuna goyon bayansu ga hakan, Mista Shehu yace gwamnatin bata yi adawa da hakan ba sai dai akwai hanyoyi daban-daban da wadanda ke goyon haka suka zo da shi.

Ya bayyana a shirin Channels TV na ranar yanci cewa, “Tabbas akwai sake fasalin lamuran kasa a manufofin jam’iyyarmu, sai dai ina tunanin bambancin gwamnati da na wadanda ke goyon hakan ita ce tsarin cimma manufar.”

A cewar shi, yawancin masu goyon bayan sake tsarin ne da zai kasance mai zaman kanta, ba tare da hannun majalisar dattawa ba a ciki.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa (hotuna)

Amman gwamnatin ta yarda cewa duk wani abu da ake nufin ware majalisa a ciki ba wakilcin ra’ayin mutane bane.

A wani lamarin kuma, mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba, ya jagoranci zaman majalisar zartarwa da ake yi a kowani mako. An fara zaman majalisar ne misalin karfe 11 na safe a fadar shugaban kasar, Abuja.

Daga cikin wadanda suka halarci zaman majlisan harda mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel