Jihar Kwara: Mu har yanzu ko da N18, 000 ba a soma biyan mu ba - NLC

Jihar Kwara: Mu har yanzu ko da N18, 000 ba a soma biyan mu ba - NLC

Kungiyar ‘yan kwandago na Najeriya na NLC ta reshen jihar Kwara ta bayyana halin da ‘ya ‘yan ta su ke ciki a jihar. Shugaban NLC yace har yanzu wasu ma’aikatan Kwara ba su karbar N18, 000.

Shugaban rikon kwarya na ma’aikatan Kwara, Saheed Muritala, ya bayyana wannan a Ranar 1 ga Oktoba lokacin da ya zanta da Menama labarai kamar yadda mu ka samu rahoto daga NAN.

Saheed Muritala yake cewa ma’aikatan da ke kan mataki na 7 zuwa sama a Kwara, su na karban gurgun albashi ne a jihar. A cewarsa, abin da ake biya ya sabawa tsarin yarjejeniyar da ake kai.

Muritala yace ba a taba biyan cikakken karin albashin da gwamnati ta yi tun 2011 a jihar Kwara ba. Mukaddashin shugaban ‘yan kwadagon ya roki sabon gwamnan jihar ya duba wannan lamari.

NLC ta roki gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya cika alkawarin da ya dauka a lokacin ya na yakin neman zabe, ya fara biyan cikakken karin albashin N18, 000 kafin a soma biyan N30, 000.

KU KARANTA: Dalilin dauke ofishin SIP daga karkashin kulawar Osinbajo

Kwamred Muritala yake cewa: “Abin da mu ka sani a Kwara wanda ya shafe mu shi ne ayi maza a dabakka tsarin biyan N18, 000 a matsayin mafi karancin albashi ga kowane ma’aikacin jihar.”

“A nan ba mu samun sabon tsarin mafi karancin albashin da aka yi. Abin da ke kasa wani gurgun tsarin albashi ne musamman ga wadanda su ke kan matakin aiki na 07 zuwa sama” Inji Muritala.

“Gwamna mai-ci ya yi alkawari idan ya hau mulki zai biya cikakken albashin N18, 000 ga kowa. Ina sa ran cewa idan aka yi haka, lokacin da aka fito da sabon tsarin albashi, ba za a cuce mu ba.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel