Abba ko Ganduje?: Kotun sauraron korafin zaben gwamna ta fara yanke hukunci

Abba ko Ganduje?: Kotun sauraron korafin zaben gwamna ta fara yanke hukunci

Kotun sauraron korafin zaben gwamna da ke zamanta a unguwar Bompai, cikin garin Kano, ta fara zamanta a yau da misalin karfe 9:40 na safiyar ranar Laraba domin yanke hukunci a karar da jam'iyyar PDP da dan takarar ta na gwamna, Abba Kabir Yusuf, suka shigar domin kalubalantar nasarar da Dakta Abdullahi Umar Ganduje, dan jam'iyyar APC, ya samu a zaben gwamna da aka gudanar a watan Maris.

Babbar alkaliyar kotun, Jastis Halima Shamaki, ta fara karanta hukunci a kan korafe-korafen masu kara bayan fara zaman kotun.

An jibge jami'an tsaro dauke da makamai a harabar kotun da kewaye, musamman a kan titin Miller da Murtala Muhammad na unguwar Bompai.

Kazalika, an rufe kusan dukkan makarantun da ke makwabtaka da kotun .

Jam'iyyar PDP da dan takararta na gwamna a jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, sun garzaya kotu domin neman ta kwace kujerar gwamnan jihar Kano daga hannun Ganduje tare da mika ta gare su bisa hujjar cewa sune suka lashe zaben a zahirin gaskiya, amma aka murde musu.

DUBA WANNAN: Cuta a shirin ciyar da dalibai: Jami'an DSS sun kama shugaban APC, wasu mutane biyu a Kano

Da take zartar da hukunci a ranar Laraba, babbar alkaliyar kotun, Jastis Halima Shamaki, ta ce kotun ta yi watsi da bukatar Abba da PDP ne saboda sun gaza tabbatar da ikirarin da suka yi na cewa an tafka musu magudi a zaben gwamnan.

Jastis Shamaki ta kara da cewa jam'iyyar PDP da dan takarar ta na iya daukaka kara idan basu gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba.

Kazalika, ta ja kunnen magoya bayan 'yan takarar da jam'iyyunsu da su guji tayar da rikici tare da bayyana cewa Kano jihar ta ce ita ma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel