FG: Kafa sabuwar Ma’aikatar da aka yi ta sa SIP ta bar fadar Shugaban kasa

FG: Kafa sabuwar Ma’aikatar da aka yi ta sa SIP ta bar fadar Shugaban kasa

Bayan dogon lokaci ana ta surutun cewa an samu sabani a fadar shugaban kasa tsakanin Mai girma Muhammadu Buhari da kuma mataimakinsa Yemi Osinbajo, gwamnati ta yi fashin baki.

Ofishin SIP mai kula da tsare-tsaren da ke inganta rayuwar marasa galihu ta bayyana dalilin da ya sa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dauke ta gaba daya daga cikin Aso Villa.

Babban Jami’in da ke kula da sha’anin sadarwa a ofishin SIP na kasa, Justice Tienabeso Bibiye, shi ne ya fitar da wani jawabi mai gamsarwa game da sabon matakin da aka dauka kwanan nan.

Justice Tienabeso Bibiye yake cewa SIP ta koma karkashin sabuwar Ma’aikatar da aka kafa mai kula da harkar bada agaji da taimakon al’umma. Hakan na zuwa ne bayan ganin tasirin tsarin.

A cewar Tienabeso Bibiye, gwamnatin tarayya ta kafa ma’aikata sukutum ne da zai kula da taimakawa marasa galihu a Najeriya a dalilin irin amfanin tsare-tsaren da SIP ta dabbaka a baya.

KU KARANTA: Wani ya bani shawarar in ki karbar tayin aikin Buhari - Soludo

Babban Jami’in gwamnatin kasar ya ke cewa a tsawon wa’adin farko, SIP ta yi aiki ne daga fadar shugaban kasa ta karkashin ofishin mai girma mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

A jawabin na Tienabeso Bibiye, ya ce nasarorin da aka samu wajen dabbaka shirye-shiryen na SIP ya sa gwamnati ta ware ma’aikata guda domin wannan aiki da aka yi shekaru akalla uku a na yi.

Bibiye ya ce mutane miliyan 42 su ka amfana daga tsare-tsaren na SIP daga shekarar 2016 zuwa yanzu. Tun 2015 dai ofishin yana karkashin kulawar Yemi Osinbajo ne kafin gwamnatin nan ta zarce.

Idan ba ku manta ba wannan mataki da gwamnati ta dauka na janye wannan aiki da wasu ma’aikatu daga hannun Farfesa Yemi Osinbajo ya sa ake rade-radin ana kokarin rage masa karfi a gwamnati.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel