Ya kamata gwamnatin tarayya ta karkatar da kudaden da aka kwato zuwa ga tsaron jama’a - Jega

Ya kamata gwamnatin tarayya ta karkatar da kudaden da aka kwato zuwa ga tsaron jama’a - Jega

Tsohon shugaban hukumar zabe na kasa mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya shawarci gwamnatin Tarayya da ta yi amfani da kudaden da ta kwato a wajen inganta harkar tsaro a kasar, don fidda al’umman Najeriya daga mawuyacin halin da suke fuskanta.

Tsohon shugaban hukumar na INEC yayi magana ne a lokacin gabatar da lakcan da cibiyar Hudaibiyya ta shirya a makarantar Aminu Kano College of Legal and Islamic Studies in Kano.

Yace kowane dan Najeriya na bukatan ingantaccen rayuwa kuma hakkinne akan gwamnati da ta tabbatar da hakan.

Yace rashin sa’a ne cewa rashin da’a da mugayen dabi’un shuwagabanni ga al’umma ya sanya Najeriya cikin wani irin hali, “yayin da sauran kasashe suke kokarin kau da wannan halin daga tsarin su. Idan shugaba ya gaza, hakki ne akan al’umma dasu sauke shi daga ofis”.

KU KARANTA KUMA: Jami’an tsaro sun dakile fashin banki, sun kama mutum daya a Lagas

Jega ya kara da cewa akwai bukatan gaggawa ga Gwamnatin da shugaban kasa Buhari ke jagoranta da ta zo da matakan da zasu maganta rashin tsaroda rashin daidaituwa a fannoni daban daban na kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel