An kuma: Bata-gari sun hallaka basarake har lahira

An kuma: Bata-gari sun hallaka basarake har lahira

- Bata gari a karamar hukumar Amuwo-odofin ta jihar Legas sun halaka wani basarake

- Ganau ba jiyau, sun ce bata garin sunje daukar fansar dukan da mutanen yankin suka yi wa dan uwansu ne a ranar juma'a

- Tashin mummunar gobara a yankin ne yasa mutane suka je kai tallafi inda bata garin ya afka don ci da ceto

Wani basaraken gargajiya a Abule-Ado, karamar hukumar Amuwo-Odofin ta jihar Legas, Muritala Akogun ya rasa ransa sakamakon harin wasu 'yan ta'adda.

Akogun ya rasu a ranar Litinin bayan raunikan da maharan suka masa.

Jaridar The Nation ta gani cewa 'yan ta'addan sun tare basaraken ne a ranar Asabar inda suka sassaresa a kansa, hannayensa da fuskarsa.

KU KARANTA: Mata 5 da suka fi kasaita a Najeriya

Wani mazaunin yankin da ya samu raunika a harin yana asibiti inda yake karbar tallafin likitoci.

Kwanannan marigayin ya hau karagar mulkin sarautar Akogun na Edo.

A cewar mutane, ya yi kokarin hana bata garin kai hari ga mutanen yankin ne kafin su kashesa a ranar Asabar.

Jaridar The Nation ta gano cewa, bata garin sun zo maida martanin dukan dan uwansu da wasu 'yan yankin suka yi.

A wani cigaba kuma a yankin Abule-Ado a ranar juma'ar da ta gabata, gobara ta lashe gidajen katako da ke yankin.

A yayin da mazauna yankin ke kokarin tseratar da rayukansu da dukiyoyinsu, wasu bata gari sai suka yi amfani da damar don wawushe dukiyoyin mutanen.

A kama daya daga cikinsu da talabijin wanda ya yi yunkurin tserewa da shi.

Wasu mazauna yankin, wadanda suka gansa lokacin aika-aikar, sun kwace talabijin din tare da far masa.

A don haka ne yaje tare da gayyato 'yan uwansa don maida martani ga jama'ar yankin.

Marigayin Akogun, ya hanzarta barin wajen radin suna da ya je a Shibiri bayan da yaji labarin abinda ke aukuwa a yankin.

Majiyar ta ce ya kira wani Lawal, wanda ya zama mai fada a ji a cikin bata garin.

Kamar yadda basarake Otun na Edo ya sanar, "Lamarin ya auku ne yayin da Lawal ke kiran yaransa da su daina abinda suke aikatawa. Muna tsaye a gaban ofishin matasan Ado kuma bata garin na kusantomu. Yarda da maganar Lawal ta sa muka tsaya, bamu san suna da manufa ba. A take suka far mana."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel