Jami’an tsaro sun dakile fashin banki, sun kama mutum daya a Lagas

Jami’an tsaro sun dakile fashin banki, sun kama mutum daya a Lagas

Rundunar yan sandan jihar Lagas ta kama wani da ake zargi da hannu a wani harin banki da suka dakile a yankin Olorunshogo da ke Mushin.

An tattaro cewa mai laifin, Mahmoud Mohammed, da yan kungiyarsa, a ranar 24 ga watan Satumba da misalin karfe 3:50 na rana sun yi yunkurin yin fashi a wani banki kafin wasu jami’ai daga rundunar yan sandan Olosan karkashin jagorancin Shugaban reshen, SP Ayodele Arogbo suka dakile harin.

Punch Metro ta tattaro cewa kungiyar ta mutum hudu, wadanda suka zo kan babur biyu don fashin banki, sun fafata da yan sanda amma suka tsere da harbin bindiga.

An tattaro cewa Shugaban yan sandan reshen, wanda ya tafi wani sintiri a yankin, ya hadu da masu laifin akan baburan.

KU KARANTA KUMA: Wasu yan iska sun kashe wata mata da yarta a Kano

An tattaro cewa an kama Mohammed dauke da bindigogin gargajiya hudu da albursai 45.

Mai laifin ya bayyana cewa mambobin kungiyarsa sun kware wajen fashin bankuna da kwastamominsu a Lagas da sauran jihohi, inda ya kara da cewa sunyi nasarar yiwa mutane da dama fashi bisa ga bayanai da suke samu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel