Ba zan nemi yin tazarce ba - Buhari

Ba zan nemi yin tazarce ba - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ba zai nemi yin tazarce na uku a kujerarsa ba, mai magana da yawunsa Garba Shehu ya bayyana haka a jawabin da ya saki jiya.

Garba Shehu ya bayyana cewa ko shakka babu, shugaba Buhari zai sauka daga karagar mulki a shekarar 2023.

Yace: "Fadar shugaban kasa ta na mai kokarin fashin baki kan maganganun wasu kafafan yada labarai na cewa wasu kungiyoyin masu goyon bayan Buhari sun fara gudanar da zanga-zanga domin neman shugaba Buhari yayi tazarce karo na uku."

"Babu abinda zai sa shugaba Buhari ya nemi sauya kundin tsarin mulki Najeriya da ta bada daman takara sau biyu na kujeran shugaban kasa."

KU KARANTA: Fargaba da zato yayinda kotu ke shirin yanke hukunci kan zaben Kano da Sokoto yau

"Shugaba Buhari na kyautata zaton kammala wa'adinsa da zai kare a 2023, sannan a gudanar da zabe kuma ba zai yi takara ba."

"Babu alamun akwai yiwuwan hana haka faruwa."

"Yanada muhimmanci a sani cewa a baya wasu sunyi yunkurin canza kundin tsarin mulki domin cigaba da zarcewa karo na uku. Hakan ya sabawa kundin tsarin mulki kuma anyi watsi da shi. Haka ba zai yiwu karkashin wannan gwamnatin ba."

"Shugaba Buhari masoyin demokradiyyan ne. Yana girmama kundin tsarin mulki. Duk wani yunkurin canza tsarin wa'adi biyu ba zai yi nasara ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel