Fargaba da zato yayinda kotu ke shirin yanke hukunci kan zaben Kano da Sokoto yau

Fargaba da zato yayinda kotu ke shirin yanke hukunci kan zaben Kano da Sokoto yau

Dirama da fargaba a cikin jihohin Kano da Sokoto da safiyar Laraba yayinda kotunan zaben gwamnan jihohin ke shirin yanke hukuncin kan karar da aka shigar kan gwamna Abdullahi Umar Ganduje da gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum a jihohin sun bayyana cewa dalilan hakan shine yadda lauyoyin bangarorin biyu suka fafata a kotun zabe musamman a jihar Sokoto.

Kotun zaben jihar Kano za ta yanke hukunci kan karar da Injiniya Abba Kabir Yusuf da jam'iyyarsa, Peoples Democratic Party (PDP) suka shigar domin kalubalantar nasarar gwamna Abdullahi UMar Ganduje na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

A ranar Litinin, Kwamitin Alkalan karkashin jagorancin Alkali Halima S Muhammad, ta alanta cewa a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba za'a yanke hukunci.

KU KARANTA: Ba zan nemi yin tazarce ba - Buhari

A jihar Sokoto kuwa, Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC na kalubalantar nasarar gwamna Aminu Waziri Tambuwal na PDP.

Kotun zaben karkashin jagorancin Alkali Abbas Bawale ta zabi yau Laraba domin yanke hukunci.

Yayinda za'a raba gardama tsakanin Abba da Ganduje a jihar Kano, an mayar da Tambuwal da Aliyu birnin tarayya Abuja saboda tsoron tashin hankalin da ka iya faruwa bayan sanar da sakamakon.

Ku kasance tare da mu domin samun labarin yadda abin ke wakana da duminsa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel