Wani ya kira ni ya ce mani "Ka ajiyewa Buhari aikinsa saboda babu wani kudi" – Soludo

Wani ya kira ni ya ce mani "Ka ajiyewa Buhari aikinsa saboda babu wani kudi" – Soludo

Tsohon shugaban babban bankin Najeriya na CBN, Charles Chukwuma Soludo ya bada labarin yadda su ka yi da wani Amininsa bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba shi wani aiki.

Farfesa Charles Chukwuma Soludo yake cewa Abokinsa ya kira sa a waya da jin labarin cewa an nada shi cikin majalisar da za ta rika ba shugaban kasa shawara a game da harkar tattalin arziki.

Wannan Abokin na sa ya nemi ya yi watsi da aikin da aka ba shi ne saboda yana ganin cewa babu wani tsoka a aikin. Farfesa Soludo ya bayyana wannan ne jiya Ranar Talata 1 ga Okotoban 2019.

Da yake jawabi a mimbarin The Platform wanda aka saba shirya irin wannan taro duk shekara a cibiyar Kiristocin nan na Covenant Christian Center da ke Garin Legas a cikin farkon makon nan.

Charles Chukwuma Soludo ya yi Allah-wadai da yadda wasu ‘Yan Najeriya ke tunani inda ya ce: “Lokacin da aka sa ni cikin ‘Yan kwamitin da za su rika bada shawara kan tattalin arziki...

KU KARANTA: 98% na mutanen da su ka nemi aikin NDLEA ba za su samu ba

“…Sai wani Aboki na ya kira ni a wayar tarho, ya yi mani magana a cikin harshen Ibo; ya ce da ni: “Ka ajiye masu aikinsu,” Sai na tambayesa ko meyasa, sai ya ce mani “Ai babu kudi a aikin.”

Tsohon gwamnan na babban bankin CBN ya ke cewa sai wannan Aboki na sa ya kuma ce: “Aikin kwamiti ne kurum.” Hakan na nufin babu komai a harkar. Soludo yace haka mutane su ke tunani.”

A jawabin na sa, Soludo ya nuna cewa tsarin mulkin da ake tafiya a kai ba zai iya cigaba da rike tattalin arzikin Najeriya ba domin kuwa kamar a gina dogon bene a kan tsohon ginin kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel