Wata sabuwa: EFCC ta bukaci karbar kadarorin wani tsohon minista

Wata sabuwa: EFCC ta bukaci karbar kadarorin wani tsohon minista

- Hukumar yaki da rashawa na bukatar gurfanar da tsohon ministan aiyuka na musamman, Kabiru Turaki

- Hukumar na zargin tsohon ministan da badakalar kudi har naira biliyan 20

- An zargi cewa ya wasakar da kudaden ne da hadin bakin wasu 'yan kwangila, ma'aikatan ma'aikatarsa da akawun sashen

A ranar Talata, jaridar Punch ta ruwaito cewa, hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta mika bukatar gurfanar da tsohon ministan aiyuka na musamman, Kabiru Turaki, akan zarginsa da take da damfarar naira biliyan 20 gaban babban kotun tarayya da ke Abuja.

Turaki, wanda ya shugabanci ma'aikatar aiyuka na musamman daga 2013 zuwa 2015 karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya fito takarar kujerar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP a 2019. Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ne ya yi nasara a kansa tun azaben fidda gwani.

KU KARANTA: Hukumar EFCC na kara tuhumar wani tsohon gwamna da wasu laifuka

Tsohon ministan shi ne na biyu a kungiyar masu bada ga Atiku akan kalubalantar nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben da ya gabata.

Takardar kotun da jaridar Punch ta samu ta wacce hukumar EFCC ke bukatar karbar kudaden wata damfara da ke da alaka da Turaki.

Jami'in bincike na EFCC, Bello Adama, ya ce hukumar ta mika bukatarta ne na kwace kudaden sakamakon rahoton sirri da ta samu akan almundahanar makuden kudi har naira biliyan 20 a yayin da Turaki yake minista.

Mai binciken ya ce, kudin an waresu ne don aiyukan yankin arewa maso gabas tare da shawo kan fadace-fadace da kalubalen tsaro da ke addabar yankin.

Ya kara da cewa, ma'aikatar ta yi yarjejeniya da kamfanoni ne don samar da kayayyakin da suka hada da babura, takin noma da Keke Napep amma sai ministan da mukarrabansa suka yi amfani da kwangilar wajen wafce kudin.

Takardar ta yi bayani kamar haka: "A watan Janairu na 2018, hukumar EFCC ta samu bayanin sirri yadda tsohon ministan aiyuka na musamman, Kabiru Turaki, ake zargin ya hada kai wajen almubazzarantar da dukiyar mutane har naira biliyan 20 wacce aka ware don aiyukan yankin arewa maso gabas, tattaunawa da sasanta fadace-fadace da shawo kan tsaro a yankin."

"Cewa binciken da aka gabatar ya bayyana cewa tsohon ministan ya hada kai da wasu 'yan kwangila, ma'aikatan ma'aikatarsa da bangaren kudi don waskar da kudaden."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel