Ana yankewa wasu 'yan Najeriya daurin shekaru 1,000 a Ghana - Umahi

Ana yankewa wasu 'yan Najeriya daurin shekaru 1,000 a Ghana - Umahi

- Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya koka kan yadda rashin hakuri ke sanya wasu 'yan Najeriya barin kasar

- Gwamnan ya ce an sanar da shi cewa akwai wasu 'yan kasar da ake yankewa hukuncin shekaru 500 zuwa 1000 a kasashen ketare

- Gwamnan ya shawarci 'yan Najeriya su rika zama a gida domin bayar da gundunmawarsu wurin gina kasa

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi a ranar Talata ya ce akwai wasu 'yan Najeriya da aka yankewa hukuncin shekaru 500 zuwa 1,000 a gidajen yarin kasar Ghana da wasu kasashe.

Gwamnan ya kara da cewa kwadayin neman dukiya da rashin girmama al'adun mu na Najeriya da wasu 'yan kasan ke yi na ya sanya suka bazama zuwa wasu kasashen duniya inda suka shiga halin 'da na sani'.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe hatsabibin mai garkuwa da mutane 'Iblis'

The Punch ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin bikin cika shekaru 59 da samun 'yancin kan Najeriya da aka gudanar a filin motsa jiki na Pa Uruta Ngele da ke Abakaliki.

Ya ce, "Ya kamata 'yan Najeriya su yi wa kansu karatun ta natsu saboda irin yadda ake yi musu a kasashen waje.

"Mutane da dama suna kira ta daga Ghana suna fada min cewa ana yankewa mutanen mu hukuncin shekaru 500 zuwa 1,000 a gidajen yari."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel