2023: Watakila ‘Yan adawa su dunkule su fitar da ‘Dan takarar gamayya - Jam'iyyar NCP

2023: Watakila ‘Yan adawa su dunkule su fitar da ‘Dan takarar gamayya - Jam'iyyar NCP

Tsohon shugaban majalisar jam’iyyun Njeriya na IPAC, Dr. Yunusa Tanko, ya bayyana cewa wasu jam’iyyun adawa za su hada-kai su fitar da ‘dan takara guda domin su nemi mulki a zaben 2023.

Dr. Yunusa Tanko wanda ya taba takarar shugaban kasa a Najeriya yake cewa ‘yan adawar za su fito da ‘dan takarar gamayya ne zabe a mai zuwa domin su jarraba sa’a a takarar shugaban kasa.

A cewar shugaban jam’iyyar adawar ta NCP kasa, ‘yan Najeriya za su ga an fito da ‘yan takarar da za su iya doke jam’iyyar APC mai mulki da babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a babban zaben.

Tanko ya fadawa 'yan jarida wannan ne a lokacin da ya zanta da su wajen bikin da jam’iyyar NCP ta shira ya cika shekaru 25 da kafuwa. An yi wannan biki ne Ranar Talata, 1 ga Okotoban 2019.

KU KARANTA: Jam'iyyun Najeriya duk kanwar ja ce inji sabon Sanatan APC

“Babu shakka wasu jam’iyyun siyasar za su hada-kai su fito da karfinsu, shiyasa tun yanzu mu ka fara kira da a gyara harkar zabe yadda zuwa 2023, mun yi abin da ya dace, na samun karbuwa.”

Tanko ya kara da: “NCP jam’iyya ce mai zaman kan ta; ta na kunshe da akidar siyasa da babu mai irinta. Mu na sha’awar hadin-kai. Amma wannan bai nufin ba za mu iya yin garambawul ba.”

“Shiyasa mu ke cewa idan ana so a samu nasara, dole a tsara yadda za a rika samun wakilci daidai gwargwado a tsaron zabenmu. Mu na kallon yadda siyasar mu ta koma ta kudi da rikici.”

‘Dan siyasar ya kuma koka da yawan sauya-sheka da ake yi daga wannan jam’iyya zuwa wancan. Don haka yake ganin idan har aka yi gyara za a rage wannan da kuma rage tasirin kudi a siyasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel