Cuta a shirin ciyar da dalibai: Jami'an DSS sun kama shugaban APC, wasu mutane biyu a Kano

Cuta a shirin ciyar da dalibai: Jami'an DSS sun kama shugaban APC, wasu mutane biyu a Kano

Jami'an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) a Kano sun cafke shugaban hukumar CRC (Committee Reorientation Council Chairman) a karamar hukumar Madobi, Alhaji Sanusi Yola, mataimakinsa, Abdulkarim K. Jubril, da shugaban jam'iyyar APC na yankin, Surajo Usman Kubarachi, bisa zarginsu da tafka badakala a cikin shirin ciyar da dalibai kyauta.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa wata majiya mai kwari a cikin hukumar DSS ta sanar da ita cewa mutanen uku na amsa tambayoyi bisa zarginsu da cutar mutanen da aka dauka aikin girka abincin da za a bawa daliban firamare a yankin.

Solacebase ta ce ana zargin mutanen uku da tursasa masu aikin girka abinci basu N22,000 daga cikin N32,000 da ake biyansu duk bayan sati biyu domin su girka abincin da za raba wa daliban makarantu a yankin.

Wata majiya ta ce mutanen sun cire sunayen masu aikin girka abincin da suka ki amincewa da wannan tsarin.

DUBA WANNAN: Singham, tsohon kwamishinan 'yan sanda a Kano ya samu mukami a gwamnatin APC

"Misali, a mazabar Kanwa an dauki masu girki 22, amma sai aka cire wadanda suka ki amincewa da mayar da kudin da ake biyan su. Yanzu haka masu girki a mazabar su 4 ne kacal, duk sauran an cire sunansu daga CRC," a cewar majiyar.

Majiyar ta kara da cewa bayan masu girkin sun koma su hudu ne a mazabar Kanwa sai jama'a suka fusata tare da fara tambayar ya ake yi da kudin sauran ma'aikata 18 da ake turo wa, ina ake kai su?.

Bayan iyayen yara sun fuskanci an samu raguwar yawa da nagartar abincin da ake bawa yaransu a makarantu, sai suka kira taro domin tattauna wa a kan lamarin, wanda hakan ne ya jawo hankalin jami'an hukumar DSS har ta kai ga sun kama mutanen domin su amsa tambayoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel