EFCC ta kama ma'aikatan hukumar INEC hudu a Zamfara

EFCC ta kama ma'aikatan hukumar INEC hudu a Zamfara

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) reshen jihar Sokoto ta cafke wasu ma'aikatan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) su hudu, a jihar Zamfara, bisa zarginsu da almundahana.

Jami'an na INEC da EFCC ta kama sune; Sidi Aliyu, Hussain Jafar, Abdullahi Yusuf Abubakar da Abdulmumin Usman.

Hukumar EFCC ta ce ta kama jami'an na INEC ne bisa zarginsu da hada kai, cin amana da kuma karkatar da kudin ma'aikatan wucin gadi da yawansu ya kai miliyan N84.7.

Abdullahi Nasiru, wanda ya shigar da korafin jami'an a ofishin EFCC amadadin sauran ma'aikatan INEC na wucin gadi, ya ce an hana su N6,000 kudin alawus din abun hawa a zabuka biyu da aka gudanar a cikin shekarar 2019.

Kazalika, ya yi zargin cewa akwai banbanci a kan adadin kudin aikin zabe da aka biya su a jihar Zamfara idan aka kwatanta da sauran jihohi.

DUBA WANNAN: Gwamnoni 3 da ministoci 7 da za su raka Buhari kasar Afrika ta Kudu

Wani bincike ya nuna cewa an biya ma'aikatan wucin gadi a Zamfara N9,000 yayin da a sauran jihohi irinsu Sokoto, aka biya su N12,000.

Wani bincike da hukumar EFCC ta gudanar ya gano cewa ba a biya wasu rukunin ma'aikatan wucin gadi (presiding officers) hakkokinsu ba, jimillar hakkin kowanne ma'aikacin wucin gadi daga cikinsu ya kama N84,696,000.

EFCC ta ce tana kokarin ganin yadda za ta kwato kudaden da ma'aikatan hudu da wasu turawan zabe a kananan hukumomi 14 suka karkatar.

Hukumar EFCC ta ce za ta gurfanar da ma'aikatan da zarar ta kammala bincike, kamar yadda yake a cikin jawabin da kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya fitar.

EFCC ta kama ma'aikatan hukumar INEC hudu a Zamfara
EFCC ta kama ma'aikatan hukumar INEC hudu a Zamfara
Asali: Twitter

EFCC ta kama ma'aikatan hukumar INEC hudu a Zamfara
EFCC ta kama ma'aikatan hukumar INEC hudu a Zamfara
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel