Gwamna Yahaya Bello ya daukarwa ma’aikatan jiharsa wani babban alkawari

Gwamna Yahaya Bello ya daukarwa ma’aikatan jiharsa wani babban alkawari

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ba ma’aikatan gwamnati da yan fansho a jihar alkawarin biyansu albashi akan lokaci.

Gwamnan wanda ya fadi hakan a ranar Talata, 1 ga watan Oktoba, yayinda yake jawabin zagayowar ranar yancin kai, ya jaddada cewa lamarin rashin biyan albashi da fansho ya zama tarihi domin gwamnatinsa ta yi nasarar cika alkawarinta na biyan kudin kafin ya kure.

Gwamnan ya bayyana cewa a watannin Agusta da Satumba 2019, an biya ma’aikata kudin albashi kafin karshen wata.

Ya cigaba da cewa bisa ga tsare-tsaren da aka yi da hukumar kudi na jihar, za a biya albashin ma’aikatan daga ranar 25 ga kowani wata.

KU KARANTA KUMA: Dukkanin jam’iyyun siyasar Najeriya zamu ne ta tadda muje - Shekarau

A wani labarin kuma mun ji cewa hugaban kwamitin majalisar dattawa a kan harkokin tsaro, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi kira ga ‘yan Najeriya da cewa su bai wa Shugaba Muhammadu Buhari hadin kai domin ya samu damar cikan burinsa na kai Najeriya zuwa ga mataki na gaba.

Wannan maganar na kunshe ne cikin jawabin sanatan na muranr cikan Najeriya shekaru 59 da samun ‘yancin kai.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel